11 Agusta 2020 - 10:16
​Lebanon: Majalisar Ministoci Ta Sanar Da Yin Murabus

<p "="">A cikin wani jawabi da ya gabatar ba da jimawa ba, firayi ministan kasar Lebanon Hassan Diyab ya sanar da yin murabus din gwamnatinsa.

ABNA24 : Jawabin nasa wanda ya gabatar kasa da sa’oi biyu da suka gabata, firayi ministan kasar Lebanon Hassan Diyab ya bayyana cewa, wasu wadanda suke da hannu kai tsaye wajen rusa Lebanon, sun yi ta kokarin dora abin da ya faru a kan gwamnati, alhali su ne ummul haba’isin dukkanin abin da ya faru.

Diyab ya ce wadanda suke zargin gwamnati, su ne manyan wadanda suka hana ruwa gudua kasar, su ne a kan gaba wajen assasa cin hanci da rashawa a kasar, da kuma karya tattalin arzikinta da jefa jama’a cikin matsalolin rayuwa tsawon shekarun da suka kwashe suna rike da madafun iko a kasar.

<p "="">Ya ce gwamnatinsa tana yin kokari matuka wajen ganin an samo mafita kan lamarin, da kuma gudanar da bincike na adalci, amma kuma a lokaci guda matakin da wasu suke dauka na neman mayar da hannun agogo baya a kasar, a kan hakan ya yi murabus daga kan mukaminsa, kamar yadda kuma majalisar ministoci ta yi murabus baki daya.

342/